Monday

Home Iran ta saka wa wasu kamfanunnukan Amurka Guda15 TakunkumiIran ta sanar da cewa, za ta saka wa wasu kamfanunnukan Amurka 15 takunkumi sakamakon yadda suke ba wa Isra'ila taimako wajen aikata ta'addanci.

Sanarwar da aka fitar a shafin yanar gizon ma'aikatar harkokin waje ta Iran na cewa, takunkumina bangare 1 da Amurka ta saka wa Iran ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Sanarwar ta ce, daga ranar 21 ga watan Maris din 2017 kamranonin Amurka 15 da ke aiyukan gini da samar da makamai a Isra'ila sun shiga jerin sunayen kamfanunnukan da aka saka wa takunkumi a Iran. An hana kamfanonin mu'amala da 'yan kasar Iran kuma ba za su shiga kasar ba.

Sanarwar ta ce, sakamakon taimakon aikata ta'addanci da wadannan kasashe ke ba wa ısra'İla ne ya sanya aka saka musu takunkumin. Wasu daga cikin kamfanunnukan sun ne: Bent Tal, United Technologies Products, ITT Corporation, Raytheon, Re/Max Real Estate, Magnum Research Inch., Oshkosh Corporation, Kahr Arms da Elbit System.
No comments:
Write Comments