Wednesday

Home Jami'an Tsaro sun bakunci lahira sakamako Fashewar wani bom a jihar borno.

Boko Haram: 'Yan kato da gora sun rasu a wani
hadarin bam

Jami’an tsaro sun bakunci lahira sannan kuma
wasu su ka jikkata a lokacin da wani bam ya
tashi a Garin Dikwa da ke Jihar Borno

A daidai kan hanyar Maiduguri a Garin Dikwa ne
wani bam ya tashi inda Jami’an tsaro har 2 su
ka ce ga Garin ku nan. Haka kuma wasu mutane
kusan 3 su ka jikkata a yayin da aka taka wani
bam da ‘Yan Boko Haram su ka dasa.
Wannan mummunan abu ya faru jiya ne a Jihar
Borno kamar NAIJ.com ke samun labari. Irin
bam din nan na taba-ya-tashi ne yayi sanadiyar
mutuwar ‘yan kato da gora a Garin Dikwa yayin
da su ka shiga farautar ‘Yan Boko Haram.


Wani Dan kato da gorar yace wannan abu ya faru
ne bayan sun yi nasara kan wasu ‘Yan Boko
Haram. A hanyar dawowa ne dai motar su ta
fada kan wani bam nan take motar ta tarwatse
inda wannan mummunan abu ya faru. Yanzu dai
ana can ana jinyar wadanda su ka raunata.
Jiya ne kuma shugaban Jami’ar NOUN Farfesa
Abdallah Uba Adamu ya bayyana cewa Fursunoni
ma suna iya karatu a Jami’ar daga gidan yari
yanzu ma dai har wani Dan kaso ya dawo zai yi
Digiri na uku.
No comments:
Write Comments