Sunday

Home › › Jamiyyar Apc Tayi Nasara a Kotun Koli.


Babban alkalin Najeriya Walter Onnoghen ya tabbatar da sahihancin zaben Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, da aka gudanar a shekara ta 2015.


Dama dai wani dan uwan tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida, mai suna Mustapha Babangida ne ya je kotun kolin Najeriya, inda ya nemi da a soke zaben gwamnan jihar Nejan domin bashi damar shiga zaben fida gwani na jam’iyyar APC.
Tunda farko dai ya ce jam’iyyar ta APC, ta hanna shiga takarar duk da cewa ya biya kudin takardan shiga takarar.

Lauyan dake kare gwamnan jihar Neja, da jam’iyyar ta APC, Yunusa Ustaz Usman, ya ce sun yi godiya ga Allah akan nasarar da suka samu, inda ya kara da cewa wanda ya shigar da karar ko tantancewa jam’iyya bai samu hayewa ba.
Manyan jami’an gwamnatin jihar Neja ne dai suka cika harabar kotun kolin a lokacin yake wannan hukunci.

Mai kalubalantar zaben gwamnan jihar Nejan dai Mustapha Babangidan bai halarci kotun ba, amma lauya mai kare shi Barrister M.N Muhammad, ya ce tunda abinda kotu ta yanke Kenan basu da ja.
No comments:
Write Comments