Wednesday

Home Jam'iyyar PDP Tace "Mun gano cewa jam’iyyar APC na yi mana bita da kulli"
Jam’iyyar PDP na bangaren Ahmed Makarfi ta ce ta gano wadansu alamu dake nuna cewa jam’iyyar APC na da hannu a rikicin da jam’iyyar take ta fama da shi.

Kakakin jam’iyar PDP na bangaren Makarfi Dayo Adeyeye yace sun gano hakan ne daga yadda wasu shugabannin jam’iyar APC suke musu shishigi a harkokin jam’iyyarsu.

Yaba da misalin cewa a makon jiya ne gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya shawarci jam’iyar PDP na bangaran Makarfi cewa su goyi bayan Sheriff.

Ya kuma ce suna da labarin cewa ministan sifuri Rotimi Amaechi ya roki wani tsohon ma’aikacin dake bada lasisi a Abuja kuma jigo a jam’iyyar mai suna John Enebeli da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar da su mara ma Sheriff baya zai basu kudade.
Enebeli ya kara da cewa sanata Sheriff da kansa ya yi masa irin wannan tayin lokacin da ya fara zama shugaban jam’iyyar.

Bayan haka ya yi kira ga jami’an tsaro da kuma mutanen da suke son zaman lafiya da demokradiya da su shawarci sanatan ya bi doka, bayan haka suna zargin jami’an tsaro da nuna goyan bayansu karara ga Ali Modu Sheriff.

Halartaccen shugaban jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff yace za’a kawo ma su gyara domin su duba irin gyare-gyaren da ya kamata ayi a shelkwatar jam’iyyar da ke Abuja a cikin hutun karshen wannan mako da ya gabata.

Yace ofisoshin jam’iyyar su na neman gyara sannan wasu sashe na ginin ofishin na bukatar sabon fenti.
Ali Sheriff yace za su dawo aiki gadan-gadan ranar Litini ko Talatan wannan makon.
No comments:
Write Comments