Thursday

Home Jerin mutanen da shugaba buhari ya nada wadanda zasu jagoranci sulhunta majalissar dattijaiYanzu haka shugaban kasa ya nada kwamiti da
za ta zauna da Majalisa domin kawo karshen
takaddamar. Mataimakin shugaban kasa Farfesa
Osinbajo ne zai jagoranci wannan kwamiti domin
sulhu da ‘Yan Majalisa kamar yadda ku ka samu
labari.

Sauran ‘Yan kwamitin sun hada da dukkanin
Ministocin kasar da su ka taba zama Sanatoci a
baya wanda sun hada da Minista Udoma Udoma,
Minista Hadi Sirika, Minista Chris Ngige, Minista
Heineken Lokpobiri da kuma Minista Aisha
Jummai Alhassan. Akwai Minista Abubakar Bwari
da kuma Minista Mustafa Baba Shehuri.

Har wa yau akwai masu ba shugaban kasa
shawara a game da harkokin Majalisa a cikin
kwamitin. Wadanda su ne dai Honarabul Kawu
Sumaila da kuma Sanata Ita Enang na Majalisar
wakilai da Dattawa.

Mai ba shugaban kasa shawara game da harkar
yaki da cin hanci Farfesa Itse Sagay yayi kaca-
kaca da Majalisar inda yace ba a taba samun
Sanatoci marasa amfani ba kuma abin da suke yi
ba komai bane face sakarci. Wannan magana dai
ta kara hura wuta rigimar.
No comments:
Write Comments