Thursday

Home Jirgi Ya gaza Tãshi Yayin da aka Gãno wani bera a ciki
Wani jirgi da ya yi shirin tashi zuwa Amurka
daga London ya kasa tashi daga filin jiragen
sama na Heathrow, bayan da aka gano wani bera
a cikinsa.Fasinjojin da ke cikin jirgin wanda ya yi shirin
tashi da misalin karfe 10:40 na safe agogon
GMT, don zuwa birnin San Francisco sun zauna
tsaf suna jiran jirgin ya ɗaga, sai kawai suka ji
sanarwar faruwar lamarin, 'wanda ba a saba gani
ba.'


Ma'aikatan jirgin sun shaida wa fasinjojin cewa
jirgi ba zai iya tashi ba idan har akwai bera a
cikinsa, don haka za a shirya musu tafiya a wani
jirgin daban.

Daga karshe dai jirgin ya tashi bayan sa'o'i hudu.
Wata fasinja mai suna Carly, ta ce, 'A lokacin da
aka yi sanarwar, sai da yawan fasinjojin suka ƙi
yarda da batun.'
Ta ce, "Bani da tabbas kan yadda lamarin ya zo
wa mutane."


Ta ce an shaida musu su cewa an samo musu
wani jirgin daban, amma dai fasinjojin sun yi jiran
sa'o'i da yawa don a bude musu wata kofar kafin
su samu damar tashi.

Wasu daga cikin fasinjojin sun bayyana yadda
suka ji da faruwar lamarin a shafinsu na Twitter.

Matt Watt ya rubuta cewa: "Yanzu aka
soke tashin jirgin da na hau don zuwa San
Francisco saboda bera ya shiga cikin jirgin. To
bai samu bisa ba ne?? #britishairways",


yayin da shi kuwa
@midlandsound A Haiku, ya rubuta
cewa: "Muna dab da tashi zuwa San Francisco,
amma akwai bera a jirgin, dole mu sauka dukkan
mu.


Ya sake rubuta: "Zan sayarwa masu shirya fim
wannan labarin. Zai iya kama da wani fim da aka
taba shiryawa na yadda aka ga maciji a cikin
jirgi."


Kamfanin jiragen sama na British Airways ya ce,
"Mun san kowa a cikin jirgin nan na son bin mu
zuwa San Francisco, amma a wannan tafiyar
akwai wani dan karamin fasinja da dole sai mun
sauke shi ya kama gabansa.

"A yanzu haka duk wata halitta mai kafa biyu
(dan adam) da ke cikin jirgin nan, za su kama
hanyar California, a yi mana afuwa sakamakon
bata lokacin da muka yi."


Hukumar filin jiragen sama ta Heathrow, ta ce ba
za ta ce komai ba kan abin da ya shafi wani
kamfanin jirage.

A shekarar 2015 ma dai an soke tashin jirgin da
wani dan wasan dambe David Haye, ke ciki,
saboda ganin bera da aka yi a cikinsa.
No comments:
Write Comments