Wednesday

Home "Kaf Kasar Nan Ba wada Ya isa ya Taka min burki" inji bukola saraki
Shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki yayi
aman wuta wannan karo inda yace babu wanda
ya isa ya hana Majalisa aikin ta ko wanene

A jiya ne wasu ‘Yan Majalisar Dattawa suka nuna
cewa za ayi ta ta kare da shugaban kasa
Muhammadu Buhari a dalilin kin sallamar Ibrahim
Magu daga EFCC. ‘Yan Majalisar su ka nuna
cewa ba za su kara tanka wata takarda da ta fito
daga hannun shugaban kasar ba.
Bukola Saraki dai ya bayyana cewa babu wanda
ya isa ya hana Majalisa aikin ta a jiya kamar
yadda majiyarmu ta samu labari. Dr. Bukola
Saraki ya bayyana wannan ne a gaban Majalisar
a zaman da aka yi bayan an gama wani kus-kus.

A dalilin Magu an shirya yaki tsakanin Majalisa
da shugaban kasa
Saraki yace babu wanda ya isa yayi wa Majalisar
wata barazana ko wanene. Sai dai shugaban
Majalisar dattawar bai bayyana ko daga ina su ke
fuskantar wannan barazana ba. An dai ja layi
tsakanin Majalisar da shugaban kasa a dalilin kin
cire Magu daga aiki.

Bukola Saraki ya kuma kira ‘yan Majalisar da ke
aikin kwamitin kasafin kudi bana da su hanzarta
domin lokaci na tafiya. Saraki yace idan har
lokaci ya kure zai dauki wani matakin kuma.
No comments:
Write Comments