Wednesday

Home Kaf kasarnan Ba wanda ya isa ya ja da Shugaba Buhari : inji farfesa sagay

An maidawa Majalisa martani a kan boren da ta
ke shirin yi.


Mai ba shugaban kasa shawara game da harkar
yaki da cin hanci Farfesa Itse Sagay yayi kaca-
kaca da Majalisar Dattawa inda yace abin da
suke yi ba komai bane face sakarci. Farfesan
yace shugaba Buhari ya fi karfin ayi masa
barazana.

Sagay dai yake cewa abin kunya ne a ce irin
Sanatocin da ake da su a Najeriya kenan. Wasu
‘Yan Majalisa dai sun nuna bacin ran su inda
suka kulla damarar kin amincewa da duk wani
sabon mukami da shugaban kasa Muhammadu
Buhari ya nada kuma zai biyo ta hannun su a
dalilin kin sallamar Magu daga EFCC.


Dama can Farfesa Sagay yace Majalisa ta ki
tabbatar da Magu ne saboda sun san irin aikin da
yake yi. Sagay yace ko sun tabbatar da shi ko ba
su yi ba, ba abin da zai canza wanda hakan bai
yi wa Majalisar dadi ba ko kadan.

Shugaban kasa dai ya turawa Majalisar sababbin
Kwamishinonin Hukumar zabe na INEC tun watan
jiya wanda har yanzu ta ki tankawa tace sai an
tsige Magu. Wasu manyan Lauyoyin kasar dai
sun ce wannan ya sabawa ka’idar aiki.
No comments:
Write Comments