Monday

Home Ko kasan cewa akwai wani daki da buhari yake shiga cikin dare bayan ya tashi daga office a kullum.


Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ashe shugaba Buhari yana aiki ne ba dare ba rana har bayan dawowar sa daga Landan inda yayi fama da rashin lafiya

Mai magana da bakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya bayyanawa gidan Rediyon pyramid na Jihar Kano cewa shugaba Buhari har a gida aiki yake yi bayan an tashi Ofis. Garba Shehu yace Buhari na da wani ofis inda yake aiki idan ya shiga daki.

Ana dai ta yada cewa shugaban kasar ba ya kammala ayyukan sa ne a Ofis tun bayan da ya dawo daga rashin lafiya. Sai dai Garba Shehu yace shugaba Buhari aiki yake yi ba kama hannun yaro har a daki bayan an tashi Ofis idan ma’aikata sun watse.,

KU KARANTA: Abba Kyari kidahumi ne - El-Rufa’i ya aika sako mai zafi ga Buhari.

Garba Shehu yace tun da shugaban kasar ya dawo har yau babu ranar da bai yi aiki ba ko sau daya. Mai magana da bakin shugaban kasar yace har a karshen mako shugaba Buhari aiki yake yi abin sa ba ruwan sa.

Jiya ne Sanata Dino Melaye yace babu yadda za ayi shugaba Buhari ya kara turo sunan Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC don kuwa akwai dokar da ta haramta hakan. Melaye yace Majalisa ba za ta kara la’akari da Magu ba a matsayin shugaban EFCC bayan ta kora sa har sau biyu.No comments:
Write Comments