Friday

Home Kotu ta yanke ma mutane 4 hukuncin kisa saboda satan wayan N10,000
Wata babban kotu a garin Ibadan ta yanke wani hukuncin ban mamaki inda ta ankewa wasu mutne 4 hukuncin kisa saboda laifin satan waya.


Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Jastis Rayo Taiwo ne ya yanke wannan hukunci a rana Juma’, 17 ga watan Maris.

Masu laifin guda hudu sune Alaba Akinola (30) Sarafa Babalola (25) Sola Kolawole (27) da Ibrahim Gbedeogun (28).

KU KARANTA: Abba Kyari kidahumi ne - El-Rufa’i ya aika sako mai zafi ga Buhari

Lauyan jihar, Mr I. O Mojoyinola, yace sun aikata wannan laifi ne a ranan 19 ga watan Yuli, 2011 a Ayekale, cikin dare.

Wannan laifi ya saba dokan sashe 1(2) na fashi da makami, na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kana kuma an yankewa wani Asuma Garuba (30) hukuncin kisa bayan an zargesa da laifin kisan wani Rasaki Ayomo a ranan 12 ga watan Satumba, 2012
No comments:
Write Comments