Tuesday

Home Kwastam Ta Kama Motocin Alfarma 13 a Gidan Sanata Barau Jibrin mai wakiltar kano ta arewa.

Sanata Barau Jibrin daga Kano wanda hukumar kwastan ta kama motocin alfarma 13 a gidansa tare da wasu kayan

Hukumar Kwastan dake yaki da fasakwaurin kaya ta Najeriya ta sanar cewa ta kama motocin alfarma goma sha uku a Kano a gidan wani Sanat tare da shinkafa da wasu kaya amma bata bayyana suna sanatan ba.

VOA tayi tattaki zuwa Majalisar Dattawan Najeriya inda ta zanta da Sanata Barau Jibrin wanda a gidansa dake Kano aka samu motocin da aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan dari biyu da casa'in da takwas.

A tattaunawar su DA VOA yace " To ai babban abu shi ne ita dimukradiya ba wanda Zai ce ya fi kowa wato sanin abun da ya dace a yi. Idan ka zo da abunka aka fada ma kan cewar wannan abun a gyara ai ba wata matsala ba ce, sai a duba a zauna..Duk wadannan abubuwa bai ma dace a zo ana magana akan wadannana abubuwa ba yanzu. Abun da ya dace shi ne muna cikin wani yanayi kamata mu hada kanmu ga baki daya muga zamu taimakawa wannan kasar. Amma a zo a zauna a dinga maganganu wadanda babu tushe, misali a bar abun da yake damun kasarmu mu je muna ta wani abu na daban. Ina ganin wannan ba daidai ba ne".
No comments:
Write Comments