Thursday

Home Majalisar ِDattawan Nijeriya Ta Amince Da Sunayen Jakadu 45, inda tayi Watsi Da Wasu Guda Biyu
Majalisar Dattijan Nijeriya ta tantance da kuma amincewa da sunayen jakadu guda 45 cikin guda 47 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar musu da su a matsayin jakadun da yake son turawa kasashe waje, to sai dai sun yi watsi da wasu 2 daga cikinsu.

Kafar watsa labaran Premium Times ta ba da rahoton cewa 'yan majalisar sun dau wannan matsayar ce bisa ga rahoton da shugabar kwamitin harkokin waje na majalisar Monsurat Sunmonu, 'yar majalisar daga jihar Oyo kuma 'yar jam'iyyar APC, ta gabatar musu bayan kwamitin ya gudanar da aikin tantance sunayen mutane 47 da fadar shugaban kasar ta gabatar musu.

Rahotanni sun ce sanatocin sun ki amincewa da nadin mutane biyu daga cikin 47 wadanda su ne Sylvanus Nsofor daga Jihar Imo da kuma Jacob Daodu daga Ondo. Rahotannin dai sun ce Sylvanus Nsofor din ya gagara karanta taken Nijeriya a lokacin da ake tantance shi kana kuma ga tsufa da ke damunsa don kuwa a cewarsu shekarunsa sun kai 82. Shi kuma Jacob Daodu sun ki tantance shi din ne saboda zargin rashawa da ake masa.

Shi dai tsohon alkali Nsofor dan shekaru 82 ya soki majalisa kan tambayarsa da aka yi ya karanta taken Nijeriya da kuma batun yawan shekarunsa inda ya bukaci su je su tambayi Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe yadda ya ke jagoranci kasar duk kuwa da yawan shekarunsa.
No comments:
Write Comments