Tuesday

Home Malamin Kimiyyar nan Hawking dan kasar Birtaniya zai tafi zuwa duniyar sama

Shahararren masanin Kimiyya dan kasar Birtaniya Stephen Hawking zai tafi zuwa duniyar sama.A sanarwar da ya bayar a yayin tattaunawa da kafar talabijin ta ITV ya bayyana shirin sa na tafiya duniyar sama karkashin kamfanin yawon bude ido na Virgin Galactic mallakar dan kasuwar Birtaniya Richard Branson.

Hawking da ke da 'ya'ya 3 ya bayyana jin dadinsa game da shirin tafiya sama kamar yadda mutumin da zai haifi yaro yake ji.

Ya ce, a baya yana tunanin babu wani da zai kai shi duniyar sama. Amma kuma Branson mai kamfanin Virgin Galactic ya ba shi damar hakan. Hawking mai shekaru 75 ya amince da wannan bukata da aka mika masa.
No comments:
Write Comments