Tuesday

Home Mamman Daura, Abba kyari, Shugaban Hukumar Dss Sun Kulla kullalliya ga shugaban Efcc ibrahim magu.Wadanda ake zargi da shirya makarkashiyar sun
hada da shugaban hukumar tsaro ta sirri, DSS,
Lawal Daura, dan uwan shugaban kasa
Muhammadu Buhari, Mamman Daura da
shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Abba Kyari,
a cewar Sahara Reporters.

Wata majiyar mai karfi daga fadar shugaban kasa
ce ta bayyana ma jaridar Sahara hakan, inda tace
manyan jami’an fadan gwamnatin suna shirya
shirin ne ba tare da sanin shugaban kasa
Muhammadu Buhari ba, inda majiyar ta shaida
ma Sahara cewa shugaba Buhari bashi da nufin
tsige Magu daga mukaminsa.

Rahoton ya nuna cewa har yanzu shugaban kasa
Muhammadu Buhari bai gamsu da rahoton
batanci da hukumar DSS ta fitar akan shugaban
hukumar EFCC Ibrahim Magu ba.

Sai dai shugaban ma’aikatan fadar gwamnati tare
da hadin bakin dan uwan Buhari, Mamman Daura
suna amfani da damansu na kusanci da shugaba
Buhari wajen ganin sun raba Ibrahim Magu da
mukaminsa na EFCC, sakamakon turjiya da
Magun ke nuna musu na kin amincewa su juya
shi yadda suke so.

“Suna amfani da damansu na kusanci da shugaban
kasa tare da rashin lafiyar shugaban Buhari don
cimma manufarsu ta ganin sun tsige Ibrahim Magu
daga mukaminsa na shugabantar hukumar EFCC.
Shugaban hukumar DSS ne ya fitar da rahoton,
inda ya samu goyon bayan Mamman Daura da
Abba Kyari. Sai dai har yanzu shugaba Buhari bai
gamsu da makarkashiyar tasu ba.”
Inji wata
majiya daga fadar shugaban kasa.

Ganin sun kasa shawo kan shugaban kasa
Muhammadu Buhari kan batun, sai suka tunkari
shugaban yansandan Najeriya IG Ibrahim Idris
daya mayar da Magu hukumar yansanda.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar ma Sahara
Reporters cewa hukumar DSS ta kammala shirin
fitar da sabon rahoton batanci akan Ibrahim
Magu don a tsige shi daga shugabantar hukumar
EFCC.

Sai dai majiyar tace: “Zasu iya samun nasara idan
suka cigaba da neman biyan bukatarsu, sakamakon
shugaba Buhari na sauraron su.''
No comments:
Write Comments