Thursday

Home MTN za ta biya wani mutumi rabin miliyan; ko ka san dalili
Kotu ta umarci kamfanin MTN ta biya
wani mutumi tãra.

MTN za ta biya wannan mutumi kusan
rabin miliyan saboda shiga hakkin sa.
Wannan mutumi yace ana cire masa
kudin ‘Callertunez’ da karfi da yaji.A jiya ne wani babban Kotu da ke zama
a Garin Ibadan ta umarci kamfanin
salula na MTN da ta biya wani mutumi
kudi saboda cire masa katin waya da
aka rika yi babu gaira-babu dalili.


An dai samu MTN da laifin cirewa
wannan bawan Allah kudi a kan kari
saboda tsarin Callertunez. Ana dai saka
kidan Caller tunez ne yayin da aka kira
mutum a waya. Sai dai Kotu tace MTN
ba ta da hurumin sakawa mutum
wannan kida na Callertunez.


Wannan mutumi da aka sakawa kidan
Callertunez ya nemi Kotu ta sa a ba sa
Naira Miliyan guda saboda shiga cikin
hakkin sa. Sai dai Kotu tace hakan yayi
yawa ta kuma nemi a biya sa N50000
sannan kuma a ba Kotu N30000 saboda
bata mata lokaci.

Sai dai Lauyan na MTN yace kamfanin
duk ba su ma san anyi ba don haka
nema Kamfanin MTN din bai tura kowa
ba a zaman.


No comments:
Write Comments