Thursday

Home Mulkin Najeriya na nema yafi karfin Buhari - inji wasu tsaffin shugabanmin Nigeria (Karanta dalili)


Wasu Tsofaffin shugabannin kasa Najeriya sun ce abinda ya faru wajen tantance Ibrahim Magu a majalisa ya nuna cewa a gaskiya Buhari bashi da cikakken iko a gwamnatinsa.Majiyar naij.com ta tattauna da wadansu tsofaffin shugabannin kasannan guda biyu kuma suka bukaci kada a baiyana sunayensu inda suka nuna bacin ransu akan yadda majalisa ta ki amincewa nadin Ibrahim Magu shugaban hukumar EFCC.

“Ta yaya za’a ce wai shugaban kasa ya aika da sunan mutum sau biyu kuma ace wai majalisa ta ki amincewa dashi saboda wata zargi da akeyi akansa wanda ba’a tabbatar ba.
“Abun da ya faru ya nuna cewa ba Buhari bane ke ainihin jan ragamar wannan gwamnati.”


KARANTA WANNAN :- MUSIC VIDEO:- Martani zuwa ga masu yiwa Buhari fatan mutuwa fullsong : DOWNLOAD NOW

Shi kuma tsohon shugaban kasa na biyu da ya tattauna da mu, yace a nashi ganin idan dai ba Buhari bane da kansa yake da hannu a wannan abu da faru a majalisa akan wanda ya zaba toh lallai akwai matsala a kan yadda ake gudanar da mulki a kasannan yanzu.

“Sai dai fa idan akwai hannun shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan abin da ya faru da Magu amma idan ba haka toh akwai wadanda suka fi karfin Buhari a gwamnatinsa”.

A dalilin abinda ya faru ina ba Buhari shawara da idan bai dauki mataki akan abubuwan da ke faruwa da wadansu ba a gwamnatinsa da wuri wuri ba to zai ko sha mamaki domin kafin ya ankara komai ya lalace.”No comments:
Write Comments