Saturday

Home Musulmi na farko da ya tsaya takarar gwamna a Amurka
Abdulrahman Muhammad Al-Sayyid mai shekaru 32 kuma likita a jihar Michigan ta Amurka ya zama Musulmi na farko da ya tsaya takarar gwamna a kasar Amurka.

An haifi Abdulrahman Muhammad Al-Sayyid dan asalin kasar Masar a shekarar 1985 a gundumar Gratiot da ke jihar Michigan ta arewacin Amurka.
A watan Satumban shekarar 2015 ne aka nada Sayyid a matsayin daraktan lafiya na na jihar karkashin shugabancin Mike Duggan.
Ya ce, "Ko shi Musulmi ne ko ba Musulmi ba ne ya yi imanin zai zama gwamnan da ya fi kowanne a jihar Michigan. Abin da na yiimani da shi na da matuykar muhimmanci a wajena saboda haka abin ya ke a wajen Amurkawa da 'yan jihar Michigan.
Idan har aka zabi Sayyid to zai zama gwamna mafi karancin shekaru a Amurka bayan Bill Clinton da aka zaba a shekarar 1978, kuma baya ga karancin shekaru Sayyid ne Musulmi na farko da zai zama gwamna a Amurka.
An dai san jihar Michigan da zama a kan gaba a tsakanin jihohin da suke nuna kyama ga Musulmi.
No comments:
Write Comments