Friday

Home Nafisa Abdullahi ta ce bata yadda a dawo da Rahma Sadau kannyood baAn jefa kori'ar yarda ko rashin yarda da dawowar
Rahma Sadau' jarumai da yawa maza da mata
sun jefa kuri'ar amincewa ko kin amincewa da
dawo da Rahma Sadau masana'antar hausa fim.
Alasan Kwalli (Bakin wake) shine mai
shugabantar kungiyar amatsayinsa na shugaban
jaruman kannywood.

majiyarmu dai ta samu labarin cewa Sani Danja
yana daga sahun gaba na masu nuna goyon
bayan dawo da jaruma Rahma Sadau. Domin
acewarsa masana'antar kannywood ta sami
koma baya tun bayan da aka kori Rahma Sadau.
Domin Rahma jarumace mai tarin masoya a
Arewaci da kudancin kasar nan.

Wasu mutane sun daina kallon hausa fim sabida
sun rasa Rahma Sadau. Kuma ba abin burgewa
bane ace uba ya kori yarsa daga masana'anta.
Duk da yake Rahma tayi laifi kuma ta amsa tayi
laifi, ya kamata a yafe mata. Domin mu ma muna
yiwa Allah laifi kuma ya yafe mana. Inji Sani
Danja.

Amma daga bangaren mata Nafisa Abdullahi ta
jefa kuri'ar kada adawo da Rahma Sadau.
Acewarta Sabida idan aka dawo da ita an nuna
son kai. Domin ashekarun baya an kori jarumai
irinsu, Kubura Dako, Safiya Musa, Maryam
Hiyana, Ummi Nuhu da sauransu, amma har
yanzu ba'a dawo da su ba. Har wasu suka yi
aure. Inji Nafisa Abdullahi.

ana nan ana saka kuri'a Rahma Sadau ta
dawo ko kada adawo da ita.
No comments:
Write Comments