Wednesday

Home Osinbajo Yayi ganawa mai muhimmanci da shugabannin soji a fadar Aso Rock

osinbajo

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa a
yanzu haka shugaban tsaro da
shugabannin sauran hukumomin tsaro na
nan na ba mukaddashin shugaban kasa
Yemi Osinbajo bayani a kan al’amarin
tsaron Najeriya.


A cewar rahoton, takaitaccen bayanin
na faruwa ne a dakin al’amura dake
fadar shugaban kasa, Aso Rock a
babban birnin tarayya, Abuja.


Ministan tsaro Mansur Dan-Ali ya ce
kudurin bayanin shine “bãrin shugaban
ayyuka da sauran shugabannin hukumomin
tsaro sunba mukaddashin shugaban kasa
bayani kan yanayin tsaro a kasar”.


Dan-Ali yace tattaunawan zai ba
hukumomin tsaro wani dama da zasu
nuna “goyon baya, tsayawa a kan aiki
da biyayya da hukumar tsaron Najeriya
ke ba gwamnati mai ci.”


Yace gwamnatin shugaban kasa
Muhammadu Buhari ta samar da goyon
baya da ake bukata ga hukumomin
tsaro da kuma taimako gurin yaki da
yan ta’addan Boko Haram da kuma
sauran abubuwan dake barazana ga
tsaro a fadin kasar.

Ya kuma ce “an samo makamai,
abubuwan sadarwa da kuma kama yan
ta’addan Boko Haram da dama”
a yakin
da suka yi.
No comments:
Write Comments