Saturday

Home RIKICIN KUDANCIN KADUNA : Shugaban kungiyar Miyetti Allah ya fede biri daga kai har wutsiya.

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Ibrahim Abdullahi yace rikicin Fulani makiyaya da mazauna garuruwan kudancin Kaduna da yaki ci yaki cinyewa rikici ne saboda rikicin ba da fulanin kasa Najeriya bane rikicin da makiya da ga kasashen waje ne.

Ibrahim Abdullahi ya fadi hakanne a lokacin da yake tattaunawa da gidan Jaridar PREMIUM TIMES a Kaduna.

“Wannan rikici da yaki ci yaki cinyewa ya shafi makiyaya ne da suke shigowa kasa Najeriya daga kasashen waje. Muna da hanyoyi uku ko hudu da makiyaya suke bi zuwa Najeriya domin kiwon dabbobinsu kuma uku da ga ciki ya yi mahada ta yankunan jihar Kaduna ne.

Yace biyu daga cikin hanyoyin nasu ya faro ne daga kasar Kamaru sannan yabi ta Kananan hukumomin Lere da da Kauru.

Sannan akwai wanda ya taso daga kasar Nijar ya biyo ta jihar Kano da Katsina sannan ya biyo ta jihar Kaduna.

Yace matsalar ta samo asali ne tun bayan rikicin bayan zaben 2011 in da aka kashe wadansu Fulani makiya ‘yan Kasar Kamaru da Chadi. An kashe musu dabbobi masu dimbin yawa sannan da wasu makiyaya sun rasa rayukansu.

Bayan haka ne fa wadanda suka tsira suka koma suka fadi abun da ya faru ga ‘yan uwansu.
Ibrahim yace bayan sun sami sakon cewa fulanin suna shirin dawo yankunan domin daukan fansa shine suka shawarci gwamnan jihar Patrick Yakowa da ya maza maza ya dauki mataki akai.
Gwamnan baiyi wata wata ba ya kafa wata kwamiti domin a tafi har can kasashen domin ganawa da wadanda aka kashe musu shanu domin biyan su diyya.

Ibrahim Abdullahi yace bayan amincewa da wannan Magana da akayi, shine ya jagoranci tawagar da da suka yi tafiyar.
Yace sun tafi har kasar Kamaru inda suka gana da daya daga cikin wanda yayi hasaran shanu sama da 200.

Yace irin makaman da ya gani an shirya su domin tunkaran kudancin Kaduna ya bashi tsoro.
Yaga makamai iri-iri da matasa masu yawa inda wadansu turawa ne ma ke horas da su dabarun yaki. Bayan ganin hakan ne sai ya shaida wa mutanen cewa ya zo ne domin isar da sako daga gwamnan jihar Kaduna.

“ Na shaida musu cewa lallai fa babu wani abun da gwamna Yakowa bazai yi domin ganin an wanye lafiya. Nace musu gwamnan ya amince da zai biya diyya shanun da sukayi hasara.”
” Suka amince da tayin da gwamna Yakowa yayi a wancan lokacin. Shine na dawo Kaduna domin in bashi bayanai akan yadda mukayi da mutanen Kamaru.


Bayan na bashi bayanan sai Yakowa yace mini hakan yayi daidai. Amma zai yi tafiya zuwa kasar Kudu idan ya dawo sai in koma kasar Chadi domin kammala wannan neman sulhu da akeyi.
Allah mai ikon sa sai baiyi zai dawo ba. Yayi hadarin jirgin sama ya rasu.

Bayan Ramalan Yero ya zama gwamna a jihar Kaduna, mun koma mun same shi kan a kammala wannan neman sulhu da marigayi Yakowa ya faro.
“ Tun da ya karbi wannan bayanai yace zai neme mu bai kara waiwayar mu ba.”
Daga Karshe, Ibrahim Abdullahi y ace cikin taimakon Allah sai El-Rufai ya zama gwamna. “ El-Rufai kuma ya amince da a ci gaba da tattaunawa daga inda Yakowa ya tsaya.
El-Rufai yace ya fara biyan makiyayan kamar yadda Yakowa ya amince zai yi daga bayanan kwamitin da ya nada kafin Allah ya dauki ransa.
No comments:
Write Comments