Friday

Home Rikicin Shugabancin Jam"iyyar Adawa ta PDP Ya zo Karshe.
A wani rahoto DA NAIJ.com ta fitar mun ji cewa Ali
Modu Sheriff da Ahmed Makarfi sun saka hannu
a wata takarda da ke nuna cewa sun sasanta.
Shugabannin PDP dai sun rattaba hannu a wata
takardar lumana da ke nuna cewa sun sasanta
wanda hakan na iya kawo karshen rikicin da ya
addabi Jam’iyyar na dogon lokaci. Ali Sheirff din
da Ahmad Makarfi dai duk kowa na ikirarin cewa
shi ne shugaban Jam’iyyar.

Gwamnan Jihar Bayelsa wanda shi aka nada a
matsayin wanda zai sasanta bangarorin
Jam’iyyar ne yayi wannan kokari. Gwamna
Dickson ya tabbatar da cewa kowa ya sa hannu
a takardar da tace babu wanda zai kara caccakar
wani.

Ali Modu Sheriff da Ahmed Makarfi sun sasanta
An dai nemi sa hannun kowane bari na
Jam’iyyar, inda Bernard Mikko na bangaren Ali
Sheriff ya sa hannu sannan kuma Prince Dayo
Adeyeye ya sa hannu a madadin bangaren
Ahmed Makarfi. Daga yanzu dai ba za a kara jin
sukar juna ba daga wani bangare.

A wannan makon kuma wani Dan Majalisa
Honarabul Hassan Anthony mai wakiltar Yankin
Jihar Benue a karkashin PDP ya tsere daga
Jam’iyyar inda ya koma Jam’iyyar APC mai
mulki. Hakan dai na karawa APC karfin rinjaye a
Majalisar Tarayya.
No comments:
Write Comments