Thursday

Home Rundunar soji Ta kai wani harin mamaya A cibiyar shi'a Dake jihar katsina.


Rundunar sojin Najeriya ta kai wata harin
mamaya gidan mabiya addinin Shi’a da ke
jihar Katsina.Kungiyar yan Shi’a tace ana cin zarafinsu bayan
harin da aka kai musu da dare a Katsina
Kungiyar yan Shi’a ta koka akan
wannan hari inda ta saki wani jawabi a
ranan Alhamis, 2 ga watan Maris.


Kungiyar tace wannan hari da ban
haushi kuma tsokana ne.
Duk da sunce babu harbin da akayi,
kungiyar tace wasu mambobinta sun
jikkata sosai bayan jami’an soji sunyi
musu dukan kawo wuka.

Sashen jawabin da kungiyar ta yi yace:

“ Soji rike da manyan makamai sun afka
cibiyar kungiyar yan Shi’a a jiya
02/03/17 cikin dare inda sukayi kokarin
ratsawa ciki kuma suka jima mambobin
kungiyarmu raunuka.

“Kungiyar IMN tace da sojin sun kawo
harin zaman lafiya ne bisa ga doka, da
basu shigo suna dukan mutane da gorori
ba. duk da cewan basu harbi kowa ba,
mutane da yawa sun jikkata.

“Kungiyar IMN ta siffanta wannan abu a
matsayin neman tsokana, wanda bai
kamata ba. shin ta wani dalili zasu shigo
cikin dare ba tare da izina ba? wanene
ya turo su kuma me suka zo yi?”


Har yanzu dai hukumar soji batayi
Magana akan wannan lamari ba.

Wannan abu na faruwa ne bayan
gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya
rattaba hannu kan wata doka na hana
wani taron gangami a jihar.
No comments:
Write Comments