Sunday

Home Sabon Makircin Majalisar Dokokin Kasar Amurka Ga Kasar IranWasu gungun 'yan Majalisun Dokokin Amurka da suka fito daga manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu Democratic da Republican sun gabatar da daftarin kuduri da ke neman tsananta kakaba takunkumi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Sabon daftarin kudurin da 'yan Majalisun Dokokin Amurka 14 da suka fito daga manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu Democratic da Republican suka gabatar, yana dauke da bukatar kakaba takunkumi mai tsauri kan wasu jami'an kasar Iran da suke da alaka da shirin samar da makamai masu linzami na kariya.

Sanata Robert Menendez daga jam'iyyar Democratic da hadin gwiwar Sanata Bob Corker shugaban kwamitin kula da siyasar harkokin wajen kasar Amurka a Majalisar Dattijan Amurka su suka tsara sabon daftarin kudurin, duk da cewa suna da'awar cewa: Sabon daftarin kudurin baya da alaka da yarjejeniyar shirin makamashin nukiliyar Iran da aka cimma da manyan kasashen duniya. Manyan mashawarta a gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump suna da tabbacin cewar wannan wata babbar damace ga gwamnatin Trump a fagen ci gaba da sanya matsin lamba kan kasar Iran matukar sabon daftarin kudurin ya samu karbuwa a Majalisar Dokokin kasar ta Amurka.

A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan an yi ta samun bullar matsalolin sabani da rabuwan kai a fagen siyasar harkokin wajen Amurka kan irin matakan da kasar ya dace ta dauka a fagen fuskantar kasar Iran. A halin yanzu haka da zaman taron shekara- shekara na kwamitin alaka tsakanin Amurka da Haramtacciyar kasar Is'ra'ila na "AIPAC" ke kara karatowa akwai yiyuwar zaman taron ya fi maida hankali kan hanyoyin kalubalantar kasar Iran. Kamar yadda a wannan lokaci Majalisar Dokokin Amurka ke son nunawa Donald Trump cewa bangaren dokoki da na zartarwa zasu iya aiki tare a fagen cimma bukatun da suka sanya a gaba musamman kan kasar Iran.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, tun bayan gabatar da wannan sabon daftarin kuduri kan neman kakaba takunkumi mai tsauri kan kasar Iran kadan ne daga cikin 'yan jam'iyyar ta Democratic suka nuna goyon bayansu ga sabon daftarin.


Wannan sabon yunkuri na wasu daga cikin 'yan Majalisar Dokokin Amurka kan neman sake kakaba takunkumi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa da'awar cewa takunkumin baya da alaka da shirin makamashin nukiliyar Iran amma a fili yake cewa yunkuri ne da ke neman yin kafar ungulu ga yarjejeniyar makamashin nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.

Tabbas gwamnatin Trump tana da masaniyar cewa babu wani bangare da yake da hakkin yin watsi da yarjejeniyar makamashin nukiliya da aka cimma kan kasar Iran sakamakon haka ta bullo da wannan sabon makircin, kuma dama tuni sabuwar gwamnatin Donald Trump ta fito da maitarta a fili kan irin mummunar adawarta kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran musamman matakin da ta dauka na sabunta takunkumin kasar Amurka na bangare guda kan Iran, ci gaba da tsare kudaden Iran a Amurka ga kuma wani sabon yunkuri na neman kakaba takunkumi kan kasar ta Iran bisa da'awar shirinta na makamai masu linzami.
No comments:
Write Comments