Saturday

Home ""Sai mun Dauki Fansa"" : Naija Delta N.D.A
Tsagerun Niger Delta sun yi
barazanar daukar fansa kan
Africa ta KuduWasu kungiyoyin tsagerun yankin Niger
Delta a Najeriya, sun yi barazanar, amfani
da bam wajen tarwatsa wasu kamfanonin
Africa ta Kudu a matsayin martani kan
barnar da akai wa ‘yan Najeriya a kasar.
Tsagerun Niger Delta sun yi barazanar daukar
fansa kan Africa ta Kudu.


Tsagerun Niger Delta dai sun baiwa
hukumomin Najeriya wa’adin wata
guda su rufe kamfanonin kasar Africa
ta Kudun ko kuma su lalata su.
Wannan na zuwa a dai dai lokacin da
majalisun Najeriya suka kafa tawagar
da zata gana da hukumomin Africa ta
Kudu kan wannan matsala.

Sai dai yayin zantawarsa da majiyar
mu, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa na sashin
nazarin kumiyyar siyasa da ke jami’ar
Bayero a Najeriya, ya ce za’a tafka
babban kuskure muddin aka ce za’a
maida martani bata hanyar lumana ba,
kan harin da wasu yan Africa ta Kudu
suka kaiwa ‘yan Najeriya.

A cewar Dr Dukawa wajibi ne awarware
matsalar ta hanyar diflomasiya, wajen
gudanar da sahihin binciken
musabbabin matsalar, a kuma tantance
zargin da ‘yan Africa ta Kudun ke wa
‘yan Najeriya bisa bata musu kasa, da
ya kunshi tu’ammuli da kwayoyi da
masha’a.

Dr Dukawa ya ce ta hanyar
Diflomasiyya ne kawai za’a tabbatar
daukar matakan adalci ga dukkanin
bangarorin da matsalar ta shafa.No comments:
Write Comments