Tuesday

Home Shugaban majalissar Dattawa Bukola Saraki Ya Gurfana a Gaban kwamitin bincike na majalissar.

Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola
Saraki ya gurfana gaban kwamitin bincike na
majalisar dattawa dake bincike kan zarginsa da
ake yin a mallakan wata motar alfarma da
hukumar kwastam ta kwace.

A watan Janairu data gabaya ne dai hukumar
kwastam ta kama motar bayan ta gano
takardunta na jabu ne, kamar yadda jaridar The
Cable ta ruwaito.

Ana zargin cewa dalilin kenan da ya sanya majalisar ta matsa
wa shugaban hukumar ta kwastam Hamid Ali,
baya rasa nasaba da kwace wannan mota da
jami’an hukumar kwastam suka yi.

A jiya Litinin 27 ga watan Maris ne tsohon
shugaban masu rinjaye Sanata Ali Ndume ya
gabatar da koke gaban majalisar akan lallai ya
kamata a bincike gaskiyar zargin da wata jarida
tayi na cewa wai an kwace motar Bukola Saraki
a tashar ruwa.

Sai dai Saraki ya bayyana ma kwamitin cewar
bashi da masaniya dangane da shigo da motar,
inda yace shi ba mai shigo da kaya bane, kuma
bai sanya wani ya shigo masa da mota a
madadinsa ba.

“Nagode ma mambobin kwamitin nan da suka
gayyace ni, na farko dai ni ba mai shigo da kaya
bane, kuma bani da wani wakili da na sanya ya
shigo min da kaya.”
Inji Saraki.

Shugaba majalisar dattawa ya bayyana cewa
lallai sanatoci sai sun dage wajen kare martabar
majalisar sakamakon akwai miyagun mutane
masu son ganin sun bata ma majalisar suna, inda
ya kara da cewa bambamcin mulkin soji dana
farar hula shine majalisun dokoki.
No comments:
Write Comments