Saturday

Home Sojoji sun kai hari kan 'yan ta'addar PKK a ciki da wajen kasar : turkiyya


Dakarun Turkiyya sun kai hare-hare kan 'yan ta'addar PKK a arewacin Iraki da kuma yankin Hakkari da ke cikin kasar inda suka lalata gine-gine 16 mallakar 'yan ta'addar.

Rahotanni sun ce, an kashe 'yan ta'adda 9 a yayin kai hare-haren.

Sanarwar da aka fitar daga rundunar sojin Turkiyya ta bayyana cewa, sojojin saman kasar ne suka kai hare-haren a yankunan Metina, Zap, Ava┼čin-Basyan, Kandil da Hakurk da ke arewacin Iraki tare da kuma wajen garin Hakkari.

A gefe guda kuma an kwace wasu kayan hada bama-bamai a farmakin da aka kai a yankin Nazmiye da ke Tunceli.

A tsakiyar garin Tunceli kuma an kai farmaki tare da kwace bindigu, kayan hada bam, bama-bamai na hannu da dama daga hanun 'yan ta'addar na PKK.
No comments:
Write Comments