Sunday

Home › › Sojojin Najeriya sun kwato motocin yaki, kuma sun fatattaki ‘yan Boko Haram {HOTUNA}


Sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan Boko Haram inda suka kwato wasu motocin yaki da Boko Haram din suka kwace a hannun sojojin kasar Nijar.
Kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ne ya sanar da wannan nasarori da sojin Najeriya din suka samu kan Boko Haram.


Ya ce bayan motocin yaki da suka kwato, sun kama baburan hawa har gudanar 70 wanda duk sun konasu.

An kwato wasu littafen addini masu yawa, bindigogi da alburusai, tutocin kungiyar, motocin hawa kiran Hilux guda biyu da dai sauransu.

Janar Sani Usman ya ce an samu nasaran haka ne a ci gaba da kakkabe sauran maboyan Boko Haram da rundunar sojin Najeriya ta ke yi a karkashin shirinta na ‘Lafiya Dole’ a dajin Sambisa.


No comments:
Write Comments