Wednesday

Home Subhanallah An gano cutar da ke damun Buhari
An gano cutar da ke damun
Buhari


Wata majiya dake kusa da shugaba
Buhari ta shaidawa jidan jaridar Sahara
Reporters ainihin cutar da ke damun shi
shugaban

Majiyar wadda bata so a bayyana sunan
ta ta bayyana cewa Buhari yana fama ne da
gyambo a cikin sa da kuma wata irin cuta
mai matsala da ake kira 'Crohn's Disease'
wadda ake dan gantawa da kumburin yan
hanji.

Majiyar ta sake jaddada cewa wannan
cutar ce ma ke hana shugaban cin abin
ci da kuma rama musamman a farkon
shekarar nan.
Majiyar ta shaida mana cewa dama dai
a shekara ta 2013 an yi wa Buhari aiki
inda aka cire masa wani bangare dake
cikin sa.

A wani labarin kuma


, tsohon shugaban
kasa Alhaji Shehu Shagari ya yabi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan
yadda ya ke kokarin ganin ya gyara
kasa Najeriya.

Shagari ya ce Buhari mutum ne mai
gaskiya, rikon amana da kishin kasa.
Yace kokarin da Buhari yakeyi
musamman wajen yaki da cin hanci da
rashawa sannan da seta Najeriya akan
tafarkin kwarai abu ne wanda ya
cancanci yabo.

Shagari ya kara da cewa dole a jinjina
ma Buhari akan yadda ya ke ta kokarin
ganin ya farfado da tattalin arzikin
kasa Najeriya da irin shirye shirye da
gwamnatinsa ta bullo dasu domin
samun nasara akan hakan.
Shagari ya fadi hakanne a yayin da
yake jawabin murnan zagayowar ranar
haihuwarsa a garin Sokoto.
No comments:
Write Comments