Wednesday

Home Tarihin Najeriya tun shekaru aru-aru da suka wuce.

Garin Badun kafin a samu mulkin yancin kai
Wani bangaren tarihi kasar da a yau tafi kowace yawan mutane a nahiyar Afirka wato Najeriya, ya nuna cewa mutanan farko da aka fara sa mu a kasar su ne kabilar Nok a wuraren Jos na jahar Plato dake Arewa maso Gabashin kasar.
Shekaru 2,000 da suka wuce kabilar Nok sun yi suna wajen amfani da karafa domin kera wasu manyan kayayyakin kawa.
Garuruwan Benue da Calabar su ne asalin kabilar Bantu da sukai hijira suka bazu zuwa Afirka ta tsakiya da kasashen kudancin nahiyar shekaru aru aru da suka wuce.
A Arewacin Najeriya, Kano da Katsina sun kafu shekaru 1000 bayan fakuwar Annabi Isa (AS).
Kodayake Daular Kanem Borno dake kusa da kogin Chadi ce ta mamaye Arewacin Najeriya har na tsawon shekaru dari shida, amma suma wadannan garuruwan sun kasance cibiyoyin kasuwanci a yankin tsakanin kabilar Berber na Arewacin Afirka da kuma garuruwan dake karkashin daular Kanem Borno.
Daular Usmaniya
A farkon karni na 19, Shehu Usman Dan Fodio ya ci yawancin garuruwan Arewacin Najeriya da yaki, inda suka koma karkashin daular Musulunci dake da shalkwatarta a Sokoto.
Masarautun Ife da Oyo na kabilar Yarabawa a kudu maso Yammacin Najeriya sun yi suna a shekarun 1400 wato karni na 15.
Bisa ga tarihin Yarabawa, Ile Ife ita ce tushen bil adama a ra'ayinsu.
A yankin Ile- Ife ne ake sassake sassaken terra cotta wanda yai suna a kusan manyan kasashen duniya.
Shekaru da dama da suka wuce akwai lokacin da masarautar Oyo a yammacin Najeriya ta fadada har zuwa cikin kasar Togo, wanda yanuna asalin dadaddiyar mu'amala da dankwan zumunci tsakanin kasashen biyu.
Ana iya cewa masarautar Benin a kudu maso Yammacin Najeriya ita ce wadda tafi kowace girma da karfi a kasar.
Tun daga karni na 15 zuwa na 19 ne masarautar Benin ta yi zamani, kuma girmanta ya kai har cikin Eko, garin da zuwan Turawan Portugal suka sauya wa suna zuwa Legas.
Ife da Benin sun yi suna ta wajen amfani da hauren giwa, katako da karafa wajen kera abubawan da suke sayarwa.
Daular Nri
Ta bangaren kudu maso Gabashin Najeriya kuma daular Nri ta samu kafuwa tun daga kusan karni na goma har zuwa shekarar 1911, abinda yasa ta kasance daular da tafi kowace dadewa a Najeriya, kuma tana karkashin masarautar Sarki ko Eze Nri ne.
Anyi ittifakin cewa garin Nri shi ne tushen al'adar kabilar Ibo.
Garuruwan Nri da Aguleri inda tarihi ya nuna nan ne asalin kabilar Ibo na cikin haular Umeuri wadanda tsatstsan sarki Eri ne.
Bayan kabilar Ibo, akwai wasu karin kabilu a yankin kudu maso Gabashin Najeriya, wadanda suka hada da Ibibiyo da sauransu.
A nan yankin ne aka samu wasu daga cikin manyan sassake-sassake kamar Igbo-Ukwu da ke da dadadden tarihi a Afirka ta Yamma.
Gabanin shigowar Turawan mulkin mallakar Najeriya, 'yan kasar na zaman lafiya da juna tare da yin harkar kasuwanci batare da kokawar neman samun arzikin kasa ko mulki ba a dukkan sassan kasar.
Kowane bangare na amfani da tsarin mulkinsa na asali domin tafiyar da harkokin shugabantar jama'arsu. Wannan ya kawo ci gaban yankunan Najeriya
No comments:
Write Comments