Sunday

Home Trump ya fadi ba nauyi game da bukatar da yakai majalissa.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya janye shirin Inshorar lafiya da ya shirya aiwatarwa a kasar.

Trump bai samu cikakken goyon bayan da ya ke bukata ba wajen warware tsarin kula da lafiya na Amurka da ake kira Obama Care ba.

Duk irin kokarin da Trump din ya yi na neman goyon bayan sauya tsarin bai samu karbuwa ba.

Shugaban majalisar wakilan Amurka Paul Ryan ya bayyana cewa, ba su ji dadin yadda aka kasa samun nasarar wannan shiri na Trump ba.

Kuri'un 'yan majalisa 216 ake bukata domin amincewa da dokar.
No comments:
Write Comments