Monday

Home Wani minista Daga cikin ministocin Buhari zaiyi Murabus.
Ministan sufurin jiragen sama sanata Hadi Sirika
ya bayyana cewa idan har ba a kammala aikin
filin jirgin Abuja ba cikin lokacin da aka dauka zai
ajiye aikin. Ministan ya bayyana haka ne a Yau
dinnan kamar yadda majiyarmu ta bayyan

An dauki makonni 6 domin gama aikin hanyar
jirgin wanda Ministan yace idan ya gaza cika
wannan alkwarai da ya dauka zai bar kujerarsa

Sanata hadi Sirika yace ba zai iya zama cikin kunya
ba bayan ya saba alkawarin da ya shafi miliyoyin
mutane.


An dai rufe hanyar Abuja a Ranar Juma’a wancan
kimanin makonni uku da suka wuce, an koma
sauka a kasar ta filin tashin jirgin na Kaduna. Minista Hadi
Sirika ya kai ziyara tare da Ministan yada labarai
Lai Mohammed domin ganin aikin da ake
yi.

Sannan kuma Sakataren gwamnatin tarayya
Babachir David Lawal ya wanke kan sa daga duk
zargin da ake masa na cewa ofishin sa ya
bada wasu kwangiloli ga kamfanin karya wanda
aka yi gaba da wasu miliyoyin kudi.
No comments:
Write Comments