Saturday

Home Wasu daga cikin Muhimman hanyoyi da Buhari yabi wajen yaki da cin hanci da rashawa
Fadar shugaban kasar Najeriya ta kara
jaddada irin muhimman manufofin
shugaba Buhari musamman ma wajen yaki
da cin hanci da rashawa inda a cikin satin
nan ne ma suka zayyan irin kudurori da
manufofi 10 da gwamnatin ta dauka don
kawo karshen cin hanci da rashawa.


Manufofin dai an bayyana su ne a
ranar Alhamis din da ta gabata a wurin
wani taron da aka gabatar wanda
kwamitin nan dake ba shugaba Buharin
shawara kan yaki da rashawa ya shirya
a Abuja.

Ga dai manufofin nan:


1. Kaddamar da shirin binciken kwakwaf
watau The Presidential Initiative on
Continuous Audit (PICA):
Bayan
kaddamar da wannan shirin ne dai sai
gashi an bankado ma'aikatan boge har
53,000 wadanda ake biya albashi.

2. Gyara a fannin kasafin kudi : Yanzu
haka dai gwamnati ta yi gyara
musamman ta yadda ake yin kasafin
kudi wanda ada yake cike da aringizo.


3. Kaddamar da asusun bai daya watau
TSA
: Tun bayan da aka kaddamar da
wannan shirin a 7 ga watan Agusta na
2015, yanzu haka dai gwamnati ta yi
nasarar rufe asusu a bankunan kasar
nan da suka kai 20,000 inda kuma aka
samu makudan kudade.

4. Yin anfanin da lambar tantancewa ta
bai daya na Bankuna watau BVN:
ita ma
wannan yayi matukar anfanin
musamman ma wajen biyan albashi
yayin da aka gano wasu ma'aikatan da
su ka kai yawan 53,000 da suke ansar
albashi da asusu da dama.

6. Shiga yarjejeniyar 'Gwamnati a fai-fai'
watau Open Government Partnership
(OGP):
Gwamnatin dai ta shiga wannan
yarjejeniyar ne a watan Yulin da ya
gabata inda yanzu haka ta kasance ta
70 cikin wadan da suka shiga.

7. Bayar da tayin 'budaddiyar gwamnati ga
jihohi':
Gwamnatin tarayya ta bayar da
tayin shiga budabbiyar gwamnati ga
jihohin kasar nan musamman ma
wadan da ke bukatar tallafi daga wajen
ta.

8. Bayar da lada ga wanda ya bankado
bayanin sirri:
Wannan sabon salon dai
tuni ya fara aiki musamman ma ganin
yadda aka fara gano makudan kudade
daga wadanda suka sace.
No comments:
Write Comments