Sunday

Home › › Wata mata a Jihar Kaduna za ta samu Naira miliyan 286 ladan tsegumi.


Matar da ta tseguntawa jami'an tsaro
maboyar miliyoyin daloli na tsohon
shugaban kamfanin man fetur na Najeriya
NNPC za ta samu ladan kimanin Naira
miliyan 289.

Rahotanni na cewa, Elizabeth Yakubu 'yar
uwa ga tsohon shugaban kamfanin mai na
NNPC wacce ta tseguntawa jami'an tsaro
inda yayanta Andrew Yakubu ya boye
miliyoyin naira da Dalar Amurka ba ta yi a
banza ba.
Matar da ta tseguntawa jami'an tsaro
maboyar miliyoyin daloli na tsohon
shugaban kamfanin man fetur na
Najeriya NNPC za ta samu ladan
kimanin Naira miliyan 289.


Rahotanni na cewa, Elizabeth Yakubu
'yar uwa ga tsohon shugaban kamfanin
mai na NNPC wacce ta tseguntawa
jami'an tsaro inda yayanta Andrew
Yakubu ya boye miliyoyin naira da
Dalar Amurka ba ta yi a banza
ba.Rahoton wanda ake ta yadawa a
zaurukan sada zumunta da muhawara
na Whatsapp na cewa, sakamamkon
tozarta ta da yayanta Andrew Yakubu
ya yi ne, ya sa Elizabeth ta tona asirinsa
dangane da inda ya boye tarin miliyoyi
naira da wasu kudaden na kasashen
waje a garin Kaduna.

Majiyar ta ci gaba da cewa, Elizabeth ta
je wurin Andrew a inda ta nemi da ya
taimaka mata da biyan kudin
makarantar yaranta amma sai ya ki,
yana mai cewa, ai shi yanzu fansho ya
ke karba ba shi da kudi.

Bayan haka ta faru sai aka yi zargin
satar tayoyin mota guda 2 daga daya
daga cikin gidajen mai biyu da ta ke
kula masa da su, a dalilin haka ne a
cewar majiyar, Andrew ya yi mata
korar kare duk da cewa kanwa ce a gari
shi.

Ganin wannan hali da ta shiga, da
kuma irin abin da dan uwan na ta yayi
mata ne, ya sa ta toni asirinsa na
miliyoyin Naira da Dala da ya boye
wanda jami'an hukumae EFCC suka
gano a makwannin da suka wuce.

Bayan an gano makudan kudaden
Andrew Yakubu ya amsa cewa na shi
ne, amma kyauta aka bashi.

Wata Kotu a Kaduna ta bayar umarnin
da a sa kudin a aljihun gwamnatin
tarayya, yayin da Andrew ya shigar da
kara a gaban kotu a inda ya ke tuhumar
halarcin yin hakan tare da bukatar da a
dawo masa da kudinsa.

A ci gaba da yaki da cin hanci da
rashawa na gwamnatin shugaba Buhari,
an amince da a ba duk wanda ya toni
asirin wani wanda ya tara dukiyar
haram wani kaso.
Ashe tsegumi ma na da ranarsa.
No comments:
Write Comments