Wednesday

Home Yadda aka nemi a kashe shugaba Buhari da guba a fadarsa


Jaridar Desert Herald tayi wani bincike inda ta
gano yadda rashin lafiyar shugaba Buhari ta
kaya da kuma yadda aka nemi a sa masa guba.
Sai dai ba za a iya cewa rahoton ya cika gaskiya
dari-bisa-dari ba


Jaridar Desert Herald a wani dogon rahoto da ta
fitar ta bayyana cewa an yi yunkurin kashe
shugaba Buhari ne kwanaki har ta kai aka zura
da shi Asibiti a Landan. Hakan ba zai zo da
mamaki ba musamman yadda shugaba Buhari
yake da makiya cikin barayin kasa da ‘yan shi’a
da masu neman kasar Biyafara.
An bayyana cewa akwai sakaci da rashin sanin
aikin tsaro a Fadar Villa har musamman mai kula
da al’amuran yau da kullum watau Sarki Abba
wanda ‘Da ne wurin Marigayi Alhaji A. Salihijo
wanda yayi aiki da Buhari a PTF. Cikin dai
wadanda ake zargi da sakaci akwai Sojoji da
sauran Jami’an tsaro Inji Desert Herald.

KU KARANTA: Abin da ya sa El-Rufa'i ya
rubutawa Buhari wasika


Kowa dai ya san shugaba Buhari ba mutum bane
mai rashin lafiya sai ga shi wannan karo sai da
aka yi ta masa karin jini. Kai bari ma dai Likitoci
ba su taba tunanin Muhammadu Buhari zai tashi
ba. Kusan abin da aka bayyana masa kenan a
lokacin da shugaban Fastocin Angilikan ya kai
masa ziyara.

Yanzu haka dai an sa tsohon Dogarin Marigayi
shugaban kasa Janar Abacha watau Hamzah Al-
Mustafa yayi bincike game da batun. Wadanda
ake zargi dai sun hada da ‘yan shi’a da wasu
abokan hamayyar shugaba Buhari da ke cikin
Villa har ma da wasu manyan Sarakuna.
No comments:
Write Comments