Wednesday

Home Yadda Nigeria Zata kasance Bayan saukar Buhari daga mulki : a cewar wani fasto
Ko kasan abin da Bishof Azogu ya ce zai faru
idan Buhari ya mutu?Bishof Udo Azogu ya ce Idan Buhari ya mutu,
Najeriya za ta kasance a cikin tsanani wahala.
Shugaban babban coci Our Sanctuary Gosple
Church, Bishof Udo Azogu ya yi gargadin cewa
allah ya kiyaye yanzu, amma idan shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya mutu, mutane masu halin
barna za su mamaye kasar Najeriya.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Azogu ya yi wannan
magana ne a lokacin da yake jawabi ikilisiyar a
wani coci a Legas, bishof ya bukaci 'yan Najeriya
da su ci gaba da addu'a ga shugaban kasar don
shawo kan kiwon lafiyarsa da kuma cin nasara
ga kalubale da yake fuskanta daga saidanun
mutanen a cikin gwamnatinsa.

Bishof ya ce shugabancin shugaba Buhari umirni
ne daga Allah.

Ya ce: ''Allah ya riga ya shirya shugaba Buhari
domin shawo kan miyagun mutanen. Idan Buhari ya
mutu, Najeriya za ta kasance a cikin tsanani
wahala.”
No comments:
Write Comments