Friday

Home Za Ayi Wa Yaran Afrika Milyan 116 Shawshawar Polio


akalla yara Miliyan 116 za a yiwa riga kafin Polio a Afrika


A wani mataki na kawar da cutar Polio ko kuma shan inna, hukumar lafiya ta duniya ta ce za'a fara wani gagarimin shiri na allura riga kafi ga yara 'yan kasa da shekara biyar sama Miliyan 116 a Afrika.

Sama da jami'an shawshawa 190,000 ne a cikin kasashe 13 na yammaci da tsakiyar Afrika zasu fara wannan aikin a mako mai zuwa.

Wannan shirin wanda shi ne irinsa mafi girma da ba'a taba tsarawa ba a Afrika na da nufin kakkabe kasashen daga sauren wannan cutar dake nakasa yara, bayan gano wasu uku dauke da ita a shekara data gabata a jihar Borno dake arewacin Najeriya.

Hukumar ta WHO ta ce tana bukatar hadin kan dukkan hukumomi da dukkan bangarorin al'umma domin cimma wannan gurin na ganin an kawar da cutar kwata kwata daga nahiyar cikin gaggawa.

Daga cikin jerin kasashen da akwai Kamaru, Chadi, Nijar, Afrika ta tsakiya da kuma Najeriya inda a arewacin kasar ake hasashen har yanzu kwayoyin cutar na yawo sakamakon gazawa na gudnar da aikin riga kafin a wasu yankuna saboda matsalar tsaro mai nasaba da Boko Haram.
No comments:
Write Comments