Wednesday

Home Za'a gina hanyar matafiya a kasa a karkashin teku : Turkiyya
A kasar Turkiyya ana gaf da fara aikin gina hanyar karkashin kasa ta matafiya a kasa a tekun birnin Istanbul.A kasar Turkiyya ana gaf da fara aikin gina hanyar karkashin kasa ta matafiya a kasa a tekun birnin Istanbul.


Idan aka kammala aikin da zai hada Uskudar da Kabataş matafiya a kasa da masu kekuna za su iya bi su tsallaka teku ta karkashin kasa.
Wannan hanya da za a fara aikinta a 'yan kwanaki masu zuwa za ta hada Marmaray da Metro. inda za a kammala ta a cikin kwanaki 600.

Za a samar da hanyar da tsarin kimiyya da fasaha na zamani mai tsaro ga al'uma, kuma za a samar da abubuwan shakar numfashi da kuma tsaron rayuka.
Za a sanya idanu kan matafiya ta hanyar amfani da wayoyin hannu.

Za a yi amfani da hotunan al'adu wajen rufe ginin hanyar ta karkashin kasa.
Hanyar na da tsawon kusan kilomita 2 kuma matafiyan za su iya amfani da na'urar tafiyar da mutane cikin sauri.
A shekarar 2019 ne ake sa ran bude hanyar tare da fara amfani da ita.
No comments:
Write Comments