Sunday

Home "Ban Aske Gashin Kaina Ba" : Jaruma Nafisa Abdullahi
Jaruma ‘yar wasan fina-finan Hausa, Nafisa
Abdullahi ta ce bata aske gashin ta ba kamar
yadda ake ta yada wa a gari.Nafisa Abdullahi ta ce bata aske gashinta ba
Nafisa ta saka wata hoton ta ba gashi a kanta
a shafin ta na Instagram inda ta yi ma hoton
lakabi da 'Na Dawo’.


Ganin yadda hoton ta ke ta yawo a shafunan
mutane a yanar gizo da irin nuna rashin jin
dadin haka da ga wasu masoyan jarumar,
Nafisa ta sanar cewa bata fa aske gashin ta.

an ruwaito cewa jarumar ta fadi
hakan ne a shafin ta na Facebook in da ta ce
wannan hoto na wani sabon shirin ta ne.

“Ban aske gashi na ba, gashi na yana nan
daram, ga masu yada jita jita wai na aske
gashi na Saboda fim.”

No comments:
Write Comments