Tuesday

Home Kotu ta aika da makafi 2 yan luwadi gidan kaso a garin Minna : Neja

Kotu ta yanke ma wasu makafi yan luwadi
zaman gidan yari shekaru uku uku
Makafin yan luwadin suna yaudarar kananan
yara da kudi don aikata ashsha dasu
Wata kotun majistiri dake zaune a garin
Minna babban birnin jihar Neja, ta yanke ma
wasu makafi su biyu hukuncin daurin
shekaru shida a gidan yari bayan ta kama su
da laifin aikata luwadi da wasu kananan yara
biyu masu shekaru 10 da 12.

Kotun ta yanke ma makafin biyu 'yan luwadi
wannan hukuncin ne a ranar Alhamis 6 ga
watan Afrilun 2017 sakamakon samunsu da
laifin cin zarafin kananan yara ta hanyar
Luwadi, sa’annan kotun bata basu zabin
biyan tara ba.

Kamfanin dillancin labaru ta Najeriya, NAN
ta ruwaito cewar Alkaliya mai shari'a Hajiya
Hauwa ta yanke masu wannan hukuncin ne
bayan wadanda ake zargi makaho Idris
Usman da makaho Abubakar Saddik sun
amsa laifin da ake zargin su da aikatawa bisa
radin kansu, daga nan ne Alkaliya ta yanke
ma kowanin su hukuncin daurin shekaru 3 a
gidan yari, kamar yadda jaridar Rariya ta
ruwaito.


Majiyar mu ta bayyana cewar jami'in
dansanda mai gabatar da kara, Abdullahi
Mayaki ya shaida ma kotun cewar wadanda
ake zargin sun aikata laifin ne tun a watan
disambar 2016, sun kuma rudi yaran ne da
kudi naira 50 da naira 100 ne sannan suka
aikata luwadin da su, inji shi.

Dansanda mai kara, Abdullahi Mayaki ya
cigaba da cewa laifin da suka aikata ya
sabawa sashi na 19 na kundin dokokin kare
hakkin yara na Jihar Neja, bisa ga doka
wadanda ake zargin za'a yanke masu
hukuncin daurin shekaru 14 ne, amma anyi
masu sassaucin hukuncin ne saboda sun amsa
laifin su sannan sun nemi sassauci daga kotu-
cewar Mayaki.

Daraktar hukumar kare hakkin yara na Jihar
Neja Barista Maryam Haruna Kolo wacce take
a kotun yayin da ake sauraron karar ta yaba
da wannan hukunci, ta kuma jinjinawa kotun
akan tabbatar da gaskiya dan gane da
wannan shari'a.

“Ina fata wannan hukuncin zai zama darasi
ga masu kokarin aikata haka anan gaba.” inji
ta.
No comments:
Write Comments