Monday

Home Muhammadu Isufu Ya Sha Alawashin Mika Mulki A 2021 : Nijar
Shugaban kasar Nijar Muhammadu Isufu ya sha alwashin mulki a shekara ta 2021 ga wani sabon shugaba da al'ummar kasar za ta zaba.
Muhammadu Isufu ya sanar da hakan ne a cikin jawabinsa na cika shekara guda a kan kujerar shugabancin kasar Nijar a wa'adin mulki na biyu.
Shugaban ya jaddada cewa, ba shi da aniyar yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar domin zarcewa kan shugabanci a karo na uku, domin kuwa a cewarsa akwai mutane da da za su iya yin aiki kamarsa.
A shekara ta 1993 Jamhuriyar Nijar ta koma kan tafarkin dimukradiyya, amma kuma an yi ta fama da juyin mulki na soji, na karshe daga ciki shi ne wanda sojoji suka yi wa tsohon shugaban kasar tamnja Mammadu a 2010,a lokacin da ya nemi canja kundin tsarin mulkin kasar domin yin ta zarce.
No comments:
Write Comments