Saturday

Home Sabon Harin Boko Haram: Sojoji 4 Sun Mutu.

sojin Nigeria


Sojojin Najeriya hudu ne suna rasa rayukansu a
wani harin kwontan bauna da ‘yan kungiyar
Boko Haram suka kai ma su a wani kauye da ake
kira Gubdori cikin yakin karamar hukumar
Dikwa a jihar Borno.


majiyarmu ta ruwaito cewa Sanarwar da wata
majiyar soji ta fitar ta ce mayakan na Boko
Haram sun bude wuta da manyan makamai
ne akan ayarin motocin soji da ke wucewa a
kauyan, yayin da shaidu ke cewa bangaren
Abou Mosab Albarnawi na kungiyar ta Boko
Haram ne ya kai wannan hari.

No comments:
Write Comments