Saturday

Home Shin ko kasam wanene ministan ilimi na Nigeria?


Bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2015, ya
nada wasu jajirtattun mutane kuma amintattu
mukamin ministocin gwamnatinsa.

Cikin wadannan ministoci da shugaban kasa ya
nada don taimaka masa da gudanar da mulki tare
da cika alkawurran daya daukan ma yan Najeriya
akwai wani bawan Allah mai suna Adamu
Adamu.

An haifi malam Adamu Adamu ne a garin Azare
na jihar Bauchi, kuma yayi karatu a jami’ar
Ahmadu Bello dake Zaria, inda ya karanci fannin
kididdiga da tsimi.

Malam Adamu Adamu kwararren
marubuci ne daya shahara wajen fashin baki kan
al’amuran yau da kullum a jaridar Daily Trust,
inda rubuce rubucensa suke fitowa a duk ranar
Juma’a.
Adamu Adamu yayi kaurin suna wajen fadin
gaskiya komai dacinta dangane da abubuwan da
suka shafi Najeriya da ma duniya gaba daya.

Adamu ya taba zama hadimin tsohon shugaban
jam’iyyar PDP Cif Solomon Lar a zamanin dayake
gwamnan jihar Filato a karkashin jam’iyyar NPP.
A shekarun baya Adamu Adamu yayi aiki tare da
shugaban kasa da Muhamamdu Buhari tun a
zamanin dayake jagorantar hukumar PTF har
zuwa lokacin daya shiga siyasa a shekarar 2003.

A shekarar 2007 Adamu Adamu ne wakilin Buhari
a yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar
a lokacin a jam’iyyar ANPP Isa Yuguda,
sanadiyyar haka Isa Yuguda ya lashe zaben.
No comments:
Write Comments