Sunday

Home Shugaba Buhari Ya Bayyana Matsayarsa Ta Karshe Akan Magu
Buhari ya yanke hukuncin karshe a kan Magu
yayinda ya yi zaman lafiya da majalisa.A yayinda shugaban kasa Muhammadu Buhari
yayi yunkurin sasantawa da majalisar dattawa,
akwai rahotannin cewa ya yanke hukuncin karshe
a kan Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban
hukumar EFCC.


An ruwaito cewa majalisar dattawa ta
dakatar da tantance kwamishinonin hukumar
zabe 27 sakamakon ci gaba da gabatar da Magu
a matsayin shugabna hukumar EFCC duk da
shawarar da majalisar ta ba shugaban kasa na
cewa a cire sa sannan a maye gurbin sa da
wani.

Buhari na kan bakar sa a kan Magu
Har ila yau dangantakar dake tsakanin majalisar
dokoki da majalisar zartarwa ta samu tangarda
sakamakon kin gurfanar wasu jami’ai a gaban
majalisar dattawa duk da sammaci da aka aika
masu.

A ranar Laraba, shugaban kasar ya shirya wata
kwamiti karkashin jagorancin mataimakin sa
Farfesa Yemi Osinbajo don duba da kawo
karshen al’amarin.
Duk da wannan, jaridar Punch ta ruwaito cewa
wata majiya a fadar shugaban kasa tace Buhari
baya da shirin cire Magu.


Majiyar ta bayyana cewa koda dai shugaban kasa
na da ra’ayin zaman lafiya, yana nan tare da
Magu.

Majiyar ta kuma ce mambobin kwamitin sulhun
sun kasance tsofaffin sanatoci wadanda zasuyi
amfani da kwarewarsu gurin kawo karshen
al’amarin.
No comments:
Write Comments