Sunday

Home Shugaba Buhari Ya Kawo Wani Sabon Tsari A Duk Ranakun Litinin Da Laraba
Majiyarmu ta samu labari cewa a yunkurin
Gwamnatin Najeriya karkashin shugaba
Buhari na gina kasar da kayan kasar an kawo
wani sabon tsari da zai sa a rika amfani da
kayan da aka yi a cikin Najeriya.
Rahotanni na zuwa mana cewa Gwamnatin
tarayya ta mayar da Ranakun Litinin da
Laraba na kowane mako a matsayin ranar sa
kayan Najeriya ma’ana wanda aka dinka a
cikin nan gida ba na wata kasa ba.

Kowa ya so na gida Inji Shugaba Buhari
Ma’ikatar sadarwa da al’uda na kasar ta
bayyana wannan a wani jawabi da ta fitar.

Wannan dai zai sa a rika yawan amfani da
kayan kasar kuma tattalin arziki ya bunkasa
da na gida. Dama dai wannan na cikin
kudirin wannan Gwamnati mai ci.

Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar
Bukola Saraki ya bayyana cewa yana bayan
shugaban kasa Muhammadu Buhari dari-
bisa-dari. Saraki ya bayyana wannan ne a
wata hira da yayi da Daily Trust.
No comments:
Write Comments