Friday

Home Shugaba Buhari ya Tabbatarwa da Ibrahim Magu kujerarsa ta Shugaban EFCC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mukaddashin
shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa
(EFCC), Ibrahim Magu zai ci gaba da zama kan
kujerarsa ta shugabancin hukumar har zuwa wa’adin
mulkin sa.
Shugaba Buhari ya yi wannan bayani ne sakamakon
rashin amince wa da Magu a matsayin ainihin
shugaban hukumar EFCC a wasu makonin da ta gabata,
.
"Ba zan dakatar da shi ba saboda ban ga laifin da ya yi
ba, kuma ina tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa ko akwai
Magu ko babu shi zan yi yaki da cin hanci da rashawa
saboda haka ku kwantar da hankalin ku.”


Za a iya tunawa a baya, shugaban kasa Muhamadu
Buhari ya gabatar da sunan malam Ibrahim Magu ga
majalisar dattijai don tantance shi a matsayin shugaban
hukumar EFCC, amma bai yi nasara ba.
No comments:
Write Comments