Monday

Home Wani Dan kasuwa ya maka bukola saraki da majalissarsa a kotu

<img src="https://i2.wp.com/media.premiumtimesng.com/wp-content/files/2015/09/Saraki-Boy.jpg">bukola saraki


An maka shugaban Majalisar dattawa da wasu
Sanatoci a gaban kotu saboda kin tabbatar da
Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar
EFCC kamar yadda majiyarmu ta samu labari
yanzu ba da dadewa ba.

Wani Dan kasuwa mai suna Raji Rasheed
Oyewumi ya shigar da karar a babban kotun
tarayya da ke Legas yace ayi watsi da tantance
Ibrahim Magu da Majalisa tayi a Ranar 15 ga
watan Maris din jiya inda ta ki tabbatar da shi.


Ibrahim magu


Mista Raji Rasheed yace Bukola Saraki da wasu
Sanatoci 10 da suka tasa Magu a gaba bai dace
ace su ne za su tantance sa ba don kuwa su kan
su Sanatocin suna dan kashi a jikin su da
Hukumar ta ke bincike.Sauran Sanatocin sun hada da Adamu Abdullahi,
Joshua Dariye, Danjuma Goje, Ahmed Yarima,
Rabiu Kwankwaso, Theodore Orji, Stella Oduah,
Jonah Jang, Aliyu Wammako da Godswill
Akpabio.
No comments:
Write Comments