Sunday

Home Wani Sanata Ya Sha Da kyar a Garin zuru Dake a Jihar Bauchi
Sanata Ibn Na’Allah ya sha da kyar a garin Zuru

Sanata Bala Ibn Na'Allah ya sha da kyar, inda
mafusatan da suka halarci wurin bada tallafin
suka yi ta ihun ba sa so a karamar hukumar
Zuru dake jihar Kebbi.

A yayin da Sanata Bala Ibn Na'Allah ya je raba
injina da babura a garin Zuru dake jihar Kebbi a
yammacin yau Lahadi, rahotanni sun nuna cewa
ya sha da kyar, inda mafusatan da suka halarci
wurin bada tallafin suka yi ta ihun ba sa so,
saboda adawar da ke tsakanin 'yan majalisar
dattijan da shugaban kasa Muhammadu Buhari.


majiyarmu ta samu labarin cewa daga bisani
jami'an tsaro sun dauke Sanatan daga wajen,
daga bisani kuma aka karo jami'an tsaro, inda
bayan zuwan su suka soma kama wasu daga
cikin matasan dake zanga-zangar.

Bayan jami'an tsaro sun kama jama'a a wurin
taron, dandazon jama'a sun yi dafifi a kofar
ofishin 'yan inda suka yi ikrarin cewa babu wanda
ya isa ya sa a rufe matsan, inda daga baya wani
na kusa da Sanatan ya zo wajen ya umarci
jami'an 'yan sandan da su saki wadandan aka
kama.
No comments:
Write Comments