Saturday

Home Wata Mata Mai Ciki Ta kone Kurmus A Hatsarin mota da ya Faru a yau asabarWata mata mai ciki da wani fasinja sun
halaka sanadiyar wata hadarin mota da ya
faru tsakanin wata mota haya mai lamba
KTW 479 XQ a jihar Legas.

majiyarmu ta samu labarin cewa motar na
tafiya kan titin gadan Maryland da ranan yau
asabar, 8 ga watan Afrilu kawai sai motan
tayi sama tana juyawa. Mutane biyu sun kone
kurmus yayinda 4 suka jikkata.

Wadanda abin ya shafa mata ne masu sayar
da kifi a Oyingbo bayan sun sayo kifi. Motan
na hanyan zuwa daga Ikeja.

Wani wanda abin ya faru a gabansa yayi bayanin cewa motar
hayar na kokarin wuce wata mota kirar
Toyota Highlander, wadanda suke gudun
wuce hankali kawai sai ta kama da wuta.
Direban da kwandasto da wasu mutane 4 ne
suka tsira daga hadarin amma da raunuka
iri-iri yayinda wadanda sua makale cikin
motan suka kone kurmus
Jami’an hukumar RSS da LASEMA sun
taimaka wajen ceton wadanda suka tsira
kuma an kaisu asibitin Ikeja.
No comments:
Write Comments