Sunday

Home Yadda Aka Hada Baki Da Obasanjo Domin Ganin Bayan Janar Abacha : inji wani tsohon soja
Ishiaya Bamaiyi ya fasa kwan abin da ya faru a
lokacin baya.
Tsohon na biyu a lokacin shugaba Marigayi Janar
Sani Abacha watau Laftana-Janar Ishaya Bamaiyi
yace su Janar Abdussalami sun san da mutuwar
tsohon dan takarar shugaban kasa MKO Abiola
wanda yace akwai abin da ya kashe sa kuma
Janar Abdussalami kadai zai iya bayani.
Hakanan kuma Janar din mai ritaya yace ba
shakka akwai hannun su Janar Obasanjo wajen
kifar da Gwamnatin Janar Sani Abacha wanda
daga karshe Marigayi Janar Abacha ya sa aka
daure su bayan bincike.

Abdussalam ya san abin da ya kashe Abiola Inji
Janar Bamaiyi.

Bamaiyi yake cewa an yi yunkurin kashe shugaba
Abacha ta hannun mataimakin sa Janar Oladipo
Diya wanda yace bai da tantama game da
wannan. Janar Bamaiyi dai yayi wadannan
bayanai ne kwanan nan kamar yadda majiyarmu
ke samun labari inda ya wanke Janar Abacha.
Kwanan nan kuma wani Dan Majalisar Wakilai
yayi kira da shugaba Buhari ya ajiye mulki a
dalilin rashin lafiya, ya kamata shugaba Buhari
ya mikawa Mataimakin sa mulkin sannan ya
nemi wani ya nada a matsayin mataimakin
shugaban kasar daga Arewa Inji sa.
No comments:
Write Comments