Sunday

Home Sheik Zakzaky Ya Raba Kayan Abinci Ga Mabukata A Zariya.
An fara rabon tallafin ne tun daga ranar
Talatar da ta gabata.Kamar yadda ya saba a duk shekara a lokaci
irin wannan watan Ramadana, jagoran
harkar musulunci a Najeriya, Shaikh
Ibraheem Zakzaky na raba kayan abinci ga
mabukata a duk lokacin da watan Ramadana
ya gabato. Kayan abincin wanda suka hada
da shinkafa, masara, gero, suga ,taliya da dai
sauran su.


A bana ma kamar kowacce shekara, duk da
Shehin Malamin na daure a hannun
gwamnatin tarayya, amma ya yi umurni da
'yan uwansa na jini da wasu ba'adin
almajiransa da a baiwa duk wadanda aka san
yana baiwa wannan tallafi a lokacin da yake
nan a duk Unguwannin Zariya. Kuma tallafin
na bana na kayan abincin ya nunka na
koyaushe yawa. Kuma tuni aka mika su ga
inda ya dace.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, dan
uwansa Sayyid Badamasi Yaqoub ne ya
jagoranci raba kayan tallafin. An fara rabon
tallafin ne tun daga ranar Talatar, 23 ga
watan Mayu da ta gabata.
Kayan abincin da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ce a
rabawa talakawa a ZariaAl'ummar da suka amfana da wannan tallafi
sun yi matukar godiya bisa wannan
karamcin da Shehin Malamin yake nuna
musu duk da kuwa yana daure, har da
mamakinsu na ganin yadda bai manta da su
ba. Tare da yi masa addu'ar fatan alheri.
Lokacin da ake raba kayan abincin

A makon da ta gabata ne dai gwamnatin
tarayya ta ce bata da niyayr musgunawa El-
Zakzaky da ake cigaba da tsarewa a birnin
Abuja. Sai dai kuma tana bashi kariya daga
barazanar da ke iya tashi sakamakon samun
'yancinsa.
No comments:
Write Comments